Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gwajin wanda shi ne irinsa na 14 tun farkon wannan shekara, na zuwa ne bayan da kasar ta yi watsi da haramcin da akayi mata na yin gwaje gwajen makamai masu linzami dake tafiya daga wannan nahiya zuwa waccen a watan Maris da ya gabata.
A watan Afrilu, da ya gabata shugaba Kim Jong-un, na koriya ta Arewa, yayin wani faretin soji ya yi alkawarin ci gaba da inganta makammanta na nulikiya.
Ba’a dai kai ga bayyana nau’in makamin da koriya ta Arewar ta harba ba, amma masana na ganin tamakar wani gargadi ne ga makobciyarta Koriya ta Kudu, inda sabon shugaban kasar Yoon Suk-yeol zai kama mulki a cikin kwanaki masu zuwa.
Mista, Yoon, ya yi alkawari yayin yakin neman zabensa yiwuwar kaiwa koriya ta Arewa harin gargadi.
342/